Al-Fatihah

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ
2 Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; الْحَمْدُ للّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
3 Mai rahama, Mai jin ƙai; الرَّحْمـنِ الرَّحِيمِ
4 Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako. مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ
5 Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa. إِيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ
6 Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. اهدِنَــــا الصِّرَاطَ المُستَقِيمَ
7 Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. صِرَاطَ الَّذِينَ أَنعَمتَ عَلَيهِمْ غَيرِ المَغضُوبِ عَلَيهِمْ وَلاَ الضَّالِّينَ
;